Friday, 29 December 2017

MUHIMMANCIN SALLAR DARE(QIYAMUL-LAI)

FASSARAR KHUDBAR JUMU'AH DAGA MASJID ABI HURAIRA AREA 2 TSAFE JIHAR ZAMFARA
DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE
Bayan mukaddimah.....
Yan uwa musulmi masu albarka yau khudbar mu zata yi magana ne game da #MUHIMMANCIN_SALLAR_DARE (kiyamul laili)
Yan uwa musulmi a makon da ya gabata munyi khuduba ne game da sallar nafila..
To yau in sha Allah Zamu yi magana ne game da Sallar Dare wato kiyamul laili.
Hakika Allah ya yabi masu yin sallar dare a cikin suratul sajadah, "ALLAH ya kan rokon sa kuma suna ciyar da abunda muka basu,  Suna tashi sallar dare,  suna da makoma ta kwarai"
Hakika saboda kaunar mu da Allah yake yi  ya bamu damar aikata ibadu kala kala har ma yakan bamu lada idan mun aikata.
Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace "Mafificiyar sallah itace sallar nafila bayan ta sai sallar dare"
Hakama Manzo sallal lahu alaihi wassalam yana cewa "Sallar da Allah yafi so itace sallar dare"
Yan uwa musulmi masu albarka lallai wannan sallar wato sallar dare tana karawa ihlasi.
Hakika tsayuwa cikin dare yana karawa bawa tsoron Allah da natsuwa, Hakama duk ranar da dan Adam yayi sallah to zaiji natsuwa da kwanciyar hankali.
Wata rana Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace ma sahabin sa "In fada maka wata hanyar alkhairi??
Sai sahabin yace eh, Sai Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace 'Ka yawaita azumin nafila, Da sadaqah domin sadaqah tana cinye zunubai kamar yadda ruwa suke kashe wuta sai kuma ka lizimci sallar dare"
Yan uwa musulmi masu albarka muhimmancin sallar dare baya misaltuwa, Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace "ALLAH yayi rahama ga wanda ya tashi yayi sallar dare"
Hakika yan uwa musulmi sallar dare tana cikin salloli masu karawa dan Adam ihklas.
Manzo sallal lahu alaihi wassalam shine baban abun koyi garemu baki daya, Hakika Manzo sallal lahu alaihi wassalam ya kasance yana tsayuwar dare har kafasun sa su fara tsagewa har Aisha radiyyallahu anha tace masa miyasa kana Manzo Allah kake Ibadah kamar haka??
Sai Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace Shin bazan zamo bawa mai godiya ba??
Yan uwa musulmi masu albarka hakika yawan yin sallar dare yana kauda bala'oi da musibuh.
Sallar Dare tana gyara halaye kuma tana gyara halaye.
Ibn hajr asqalani yace 'Ita sallar dare tana wanke zukata'
Saboda muhimmancin sallar dare Manzo sallal lahu alaihi wassalam ya hore mu da yin sallar dare inda yake cewa "NA hore Ku da sallar dare domin tana share zukata"
Hakika sallar dare tana kara lafiya da kwarin jiki,
Ina wadanda basu da lafiya likita yace sai sun rika motsa jiki duk safiya???
To ga exercise daga likitan likitoci Manzo sallal lahu alaihi wassalam idan har ka tsarkake niya to hakika Allah zai baka lafiya da yardar sa.
Ibn Salam ya ruwaito daga cewa Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace "Ku yada sallama a tsakanin ku Ku raba Sadakar abinci Ku sada zumunta kuyi sallar dare"
Duk mai kokarin sallar dare Allah zai haska zuciyar sa....
Wata rana Manzo sallal lahu alaihi wassalam yana baiwa sahabbai labari cewa "A cikin aljannah akwai wasu benaye masu tsawo ana ganin abunda ke ciki saboda tsabar hasken su a wata ruwayar har matan da suke ciki ya kwatanta, Sai wani mutanen karkara yace ya Manzo Allah wake da wadannan benayen??
Sai Manzo Allah yace na wadanda suka iya magana ne (Magana mai kyau Sadaka ce) da wanda ya sada zumunci da wanda ya yawaita azumi da wanda ya lizimci sallar dare "
ALLAH Ya umarci Manzo sallal lahu alaihi wassalam ya tashi yayi sallar dare" KA TASHI KAYI SALLAR DARE KA ROKI UBANGIJIN KA "
Manzo sallal lahu lahu alaihi yayi addu'a ga wanda ya tada iyalinsa suka yi sallar dare.
Idan mata ta tashi zatayi to tana iya tada mijinta Shima idan bai tashi ba tana iya yayyafa masa ruwa amma idan babu matsala 
Yan uwa musulmi masu albarka saboda muhimmancin sallar dare Umar bn Khaddab ya kasance yana tada iyalinsa suyi sallah a karshen dare.
Hakika ALLAH yana sauka a sulisin dare a saman duniyar nan yana cewa "INA MASU NEMAN GAFARA INYI MASU INA MASU NEMAN BIYAN BUKATA IN BIYA MASHI??"
Yan uwa musulmi a yanzu mun bar sallar dare sai a lokachin azumin ramadana.
Idan baka iya tashi da dare to kana iya yin sallar ka bayan isha'i.
Yan uwa musulmi lokachin da yakamata muyi sallar shine misalin karfe 2,3,4 domin shine sulisin dare.
A yanzu muna ganin yadda a duniyance kowa yana neman hanyar rayuwa, Kama daga bidar kudi da sauran su.
Ita lahira babu batun kudi ko wani abu hakika yakamata mu maida hankali dan lahirar mu.
Lallai kada mu kuskura shaidan yayi tasiri garemu.
Mai hankali ne wanda keyi lahirar sa tanadi kafin yaje.
ALLAH Ka taimakemu da taimakon ka ya ubangiji ka yafe mana kurakuren mu.
Ya Allah ka biya mana bukatun mu kayi rahama ga mamatan mu ya amintar damu daga abunda muke tsoro.
(Dan Adam ajizi ne Allah ka gafarta mana abunda muka yi kuskure)
©®Ibrahim Rabilu Tsafe  Alzamfari. 07064282182
Jumu'ah 10-Rabi'ul akheer-1439
29 Friday -December-2017 AB

Friday, 15 December 2017

MUHIMMANCIN NAFILAH

FASSARAR KHUDBAR JUMU'AH   DAGA MASJID ABI HURAIRAH DAKE TSAFE ZAMFARA

DAGA IBRAHIM RABILU TSAFE

A wannan makon  limam Sani Abi hurairah Tsafe ya gabatar da khudbar ne akan #MUHIMMANCIN_NAFILAH

Bayan mukaddimah......

Yan uwa musulmi masu albarka hakika gaskiyar zance shine Alqur'ani Mai tsarki, Mafi kyawun shiriya itace shiriya ta Annabi Muhammadu sallal lahu alaihi wassalam, Mafi sharrin ayyuka shine kirkirar abu ga addini.

Yan uwa musulmi masu albarka ina maku Nasiha tare da ni kaina da muji tsoron ALLAH domin jin tsoron ALLAH shine jagora ga rayuwar mu, ALLAH yana fada cikin suratul kasas cewa "WANNAN GIDAN NA LAHIRA MU SANYA SHINE GA MASU TSORON ALLAH HAKIKA AQIBA MAI KYAU ITA KUWA AQIBA MAI KYAU TANA GA MASU TSORON ALLAH"

Saboda kaunar da ALLAH keyi mana ya sanya mana abubuwa da Zamu amfana dasu, kamar nafilfili da sauransu,  Nafila ta sallah tana Matukar muhimmancin ga ibada,

Yan uwa musulmi masu albarka sallah itace abunda za'a fara bincike a gobe Kiyama, Manzo sallal lahu alaihi wassalam na cewa "Farkon abunda za'a yiwa dan Adam hisabi akanshi shine sallah idan tayi kyau to dan Adam ya dace idan kuma an samu matsala sai ALLAH ya umarci mala'iku su binciki shin akwai nafila?
Idan akwai to sai ayi amfani da ita wajen cike sallar farilla"

Haka ma a azumi da zakkah sai a diba idan akwai wakafi da sauran ibadu!!

Kenan koda a wannan hadisin muka tsaya lallai zamu fahimci cewa nafila nada matukar muhimmanci.

A wajen yin ibadar sallah ana bukatar natsuwa sosai Ibn Abbas ya ruwaito yace" Sai kana da natsuwa sannan sallahr ka zata karbu "

Yan uwa musulmi masu albarka yawan yin nafila yana sa mutun yazama abokin Manzo sallal lahu alaihi wassalam a gidan aljannah 😁

Akwai wani sahabin Manzo sallal Sallal lahu alaihi wassalam idan Annabi zai yi alwala sai sahabin ya dauki talkaman Annabi ya rike a hannunsa hakama idan Manzo sallal lahu alaihi wassalam zai yi sallah yakan tsaya har sai Annabi ya fito, Wata rana sai Manzo sallal lahu alaihi wassalam ya tambaye shi mi kake bukata inyi maka??

Sai yace ina so in zama abokin ka a gidan aljannah.....

Sai Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace to ka taimake ni da yin nafila a koda yaushe. "

Yan uwa musulmi masu albarka yawaita nafila na kara kusan tar da dan Adam ga ubangiji, ALLAH madaukakin sarki na cewa" BAWA BAZAI GUSHE YANA SUJJADAH HAR SAI NA SOSHI "

Yan uwa musulmi masu albarka yawaita yin nafila kara maka kusanci da ubangiji ALLAH

Abdullahi bn Umar ya ruwaito cewa" Kafin sallar azahar kayi raka'a 2 bayan sallar kuma kayi 2 la'asar kayi 2 bayan ta kayi 2 hakama a magrib da isha'i hakama a sallar asuba kafin ta wato sallar fajir "

Haka ma Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace" Duk wanda yake yawaita yin nafila raka'a 12 a rana ALLAH zai gina mashi gida a aljannah "

Haka ma Manzo sallal lahu alaihi wassalam yana cewa" Kuyi raka'a 2 kafin magrib ya fadi haka har sau uku amma ga wanda yake sa hali "

Haka ma Aisha radiyyallahu anha ta ruwaito cewa" Manzo sallal lahu alaihi wassalam bai taba barin nafila ba a lokachin sallar asuba ba "

Yan uwa musulmi masu albarka hadisin dake magana game da ba'a sallah bayan la'asar na nufin idan an dade da gama sallar ne.

Daga cikin nafilolin da ake bukatar yawaita aikatawa akwai sallar duha wato ita anayi ta ne da safe, Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace "Dan Adam yana da gabobi guda 360 ana bukatar a kullum kabada Sadaka kwatan kwacin haka sai sahabbai suka ce to idan baka da kudin bada Sadakar??  Sai Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace to ka tsaftace massallaci (kamar shara ko kuma dauke wani tsinke) koda ma ace ka gaza haka to kayi sallar duha "

Yan uwa musulmi masu albarka hakika addinin musulunci yana da Matukar dadi da kuma garabasa ga wani hadisi daga Manzo sallal lahu alaihi wassalam cewa

" Duk wanda ya fito daga gida yayi aikatawa zaije massallaci to ana rubuta mashi ladar aikin hajji da umrah "

Hakika yan uwa musulmi idan muka yawaita yin nafila za'a rubuta sunayen mu cikin illiyun 😁😁

Yan uwa musulmi bayan sallar asuba yana da kyau mu rika zaunawa koda awa guda ko biyu ne Muna yin tasbih domin falalar dake ciki, Hadisi daga Manzo sallal lahu alaihi wassalam na cewa "Bayan kammala sallar asuba ka zauna har rana ta fito kana da ladar aikin hajji cikakke cikakke cikakke!!

Yan uwa musulmi dole ne mu rage yawan zama ana hira ana surutu fiye da awa guda alhali zaman baida wani amfani garemu,

Imam Muslim ya ruwaito daga Manzo sallal lahu alaihi wassalam cewa "Dayanku bazai yi alwala yana jiran sallah ba face wuta ta haramta gareshi!!"

Yan uwa musulmi kunji falala mai kyau kenan masu zuwa massallaci da Wuri suna jiran limam sun samu shiga a wannan.

Sannan kuma yan uwa musulmi yana da kyau mu yawaita yin nafila a gidajen mu domin Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace "Kada mu maida gidajen mu kamar makabartu (Domin ba'a sallah a makabarta)

Manzo sallal lahu alaihi wassalam yace" Mafificin nafila itace nafillar da akayi a gida "

Yan uwa musulmi kada mu rangwantar da kawunan mu mu kashe jikin mu da hira da surutai marar sa amfani domin wallahi akwai ranar da Zamu nemi ina ma ace Zamu yi aiki koda na kwayar zarra ne!! 😷😷

Akwai falala mai yawa a cikin sallar nafila, Manzo sallal lahu alaihi wassalam "SALLAR fajir (Kafin asuba) tafi duniya da abunda ke cikin ta"


To yan uwa musulmi kunji fa......

Tabi'ai da sahabbai sun kasance idan wani yayi laifi yana zuwa yayi nafila ya roki Allah ya gafarta masa.

*Sallar nafila tana daga Darajar dan Adam a wurin ALLAH

Hakika sahabbai da Tabi'ai suna yawaita yin nafila domin tsannanin koyi da Annabi, Saboda Annabi ya karantar dasu kuma yayi a gaban su har ma ya kwadaitar da wannan ibadar.

Yawaita nafila yana kawo abubuwa kamar haka :

*Gidan mutun yana albarka

*Darajar dan Adam tana karuwa

*Yana sanya mutun yazama abokin Manzo sallal lahu alaihi wassalam a gidan aljannah.

*Nafila na zama abokiyar hira ga dan Adam a cikin kabari.

*Zai kara maka son ALLAH

*Tana maida dan Adam yazama mutanen kirki.

*Samun ladar aikin hajji da umrah

*Kankarewar Zunubai.!!

Yan uwa musulmi masu albarka a yadda duniya ta chanza a yanzu dole ne mu rungumi koyar wa Manzo sallal lahu alaihi wassalam da duk abubuwan da ya karantar damu.

ALLAH ka gafarta mana kayi mana rahama kabamu lafiya da zaman lafiya, Ya ubangiji ALLAH kayi rahama garemu ka biya mana bukatun mu ka haskaka rayuwar mu, Ameen

©®Ibrahim Rabilu Tsafe  Alzamfari. 07064282182
Jumu'ah 20-Rabi'ul auwal-1439
Friday 15-December-2017 AB